ECOWAS ta bada tallafin jin ƙai na dala miliyan 12 da 600 ga ƙasashen da ta’addanci ya addaba a 2024
Daractar ayyukan jin ƙai da kula da walwala ta ƙungiyar Dr. Sintiki Tarfa-Ugbe ta ce ƙasashen Najeriya da Burkina Faso da Mali da ke fama da matsalar ta’addanci sun samu dala miliyan 4 cikin wannan kuɗi.
Daractar ta ECOWAS ta ce suna aiki tuƙuru domin tabbatar da habbaka ayyukan jin ƙai tare da sanya ido domin tabbatar da jama’a sun amfana da ayyukansu.
A lokacin da take jawabi a Abuja babban birnin Najeriya lokacin wani taron mamallaka kafofin talabijin a Afirka ta yamma, Tarfa-Ugbe ta ce kungiyar ECOWAS na yin aiki kafaɗa da kafaɗa da kafafen yaɗa labarai a yankin.
Taron da aka yi da nufin lalubo hanyoyin da za’a haɗa hannu da samar da dabarun tabbatar da zaman lafiya a Afirka maso yamma zai taba alli da masu ruwa da tsaki domin cimma wannan muradi.
“Na sani cewar ƙasashenmu na fama da kalubale daban-daban kamar na yaƙi da ta’addanci da sauyin yanayi da matsalar abinci. Amma dukda haka kungiyarmu ta ECOWAS za ta ci gaba da baiwa kasashe mambobinta gudunmawa tare da basu ƙwarin gwiwa wurin ganin bayan waɗannan kalubale da suke fuskanta” a cewar Dr. Sintiki
Ta ce ba zuba maƙudan kuɗi kawai suke ba, suna bibiya domin tabbatar da ganin an aiwatar da shirye-shiryen nasu na jin ƙai yadda ya kamata.
Dr. Sintiki ta ce sun ziyarci ƙasashe 4 kamar Togo da Gambi da liberia domin ganin yadda ake kashe kudin da suka bayar domin taimakawa jama’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI