Ebola ta yi ajalin mutane 6 a Gini

Ebola ta yi ajalin mutane 6 a Gini

Mutane 6 sun rasa rayukansu sakamakon sake bullar cutar Ebola a Gini.

Sanarwar da Hukumar Kula da Lafiya ta Kasa ta Gini ta fitar ta ce, ya zuwa yanzu mutane 125 aka samu dauke da cutar.

Tun shekarar 2016 ba a samu mutuwa daga Ebola ba a kasar.

Bayan wata ma'aikaciyar jiyya ta mutu sakamakon kamu da cutar a ranar 13 ga Fabrairu ne ya sanya aka aiyana shiga zango na 2 na cutar a kasar.

A gefe guda, Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana za ta bayar da tallafin dala miliyan 15 don yaki da Ebola a kasashen Gini da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

A ranar 18 ga Nuwamban 2020 ne Hukumar Lafiya ta Duniya ta sanar da kawo karshen zango na 11 na annobar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, amma a ranar 7 ga Fabrairun bana cutar ta sake bulla a yankin Biena na jihar North-Kivu da ke gabashin kasar.

A watan Disamban 2013 Ebola ta yadu a Yammacin Afirka. A tsakanin 2014-2017 mutane sama da dubu 11 Ebola ta kashe a kasashen Gini, laberiya da Saliyo.


News Source:   ()