Mutane 5 sun rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.
Bayanan da Asusun Tallafa Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) suka samu daga wajen gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo na cewa karin mutum 1 ya mutu sakamakon kamuwa da Ebola a yankin Mbandaka na arewa maso-yammacin kasar.
An bayyana kai wasu mutanen 4 asibiti bayan kamuwa da cutar a yankin Wangata.
Ministan Lafiya na kasar Dr. Eteni Longonda ya aiya sake bular cutar Ebola a yankin Mbandaka inda ya nemi taimakon Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO).