Mutane 43 ne suka rasa rayukansu a jihar Equateur da ke Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo sakamakon sake bullar cutar Ebola a karo na 11.
Sanarwar da jami'an yaki da Ebola suka fitar ta ce mutane 19 a jihar Equateur da ke yamma sun sake mutuwa.
Sanarwar ta ce ya zuwa yanzu cutar ta kama mutane 100 a yankin, wanda 43 daga ciki sun rasa rayukansu. Wasu 25 kuma sun warke.
A ranar 25 ga watan Yuni ne aka sanar da kawo karshen Ebola zango na 10 a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo wanda ya faro a shekarar 2018.
A zango na 10 na cutar da ya bulla a jihohin North Kivu, Ituri da South Kivu mutane dubu 2,277 ne suka mutu daga cikin dubu 3,470 da ta kama.
Cutar Ebola da ke zanyo zubar da jini ta fara bulla a1976 a yankin Nzara na Sudan da garin Yambuku na Jamhuriyar Demokradiyar Kongo.
An bawa cutar sunan Ebola saboda ta fara bulla a kusa da kogin Ebola da ke Kongo.