Mutane 4 sun rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.
Ministan Lafiya Eteni Longondo ya shaida cewar a arewa maso-yammacin kasar akwai sabbin mutane da suka kamu da Ebola, kuma 4 daga cikinsu sun mutu.
Ministan Lafiya na yankin Arewacin Kivu Dr. Moise Kakule makonni 2 da suka gabata ya aiya kawo karshen Ebola bayan sallamar mutum na karshe daga cibiyar kula da masu dauke da cutar inda suka fara kirgen kwanaki 42.
A watan Agustan 2018 Ebola ta bulla a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, ya zuwa yanzu an samu mutane dubu 3,314 da ta kama inda dubu 2,025 daga cikinsu suka mutu.