Dutsen Nyiragongo mai aman wuta ya fashe a Kongo

Dutsen Nyiragongo mai aman wuta ya fashe a Kongo

A jamhoriyar Demokradiyyar Kongo Dutsen Nyiragongo mai aman wuta ya fashe lamarin da ya haifar da kwashe wasu al'umma mazauna wasu yankunan birnin Goma dake karkashin hadari.

An bayyana cewa Dutsen Nyiragongo ya kasance mafi aman wuta a nahiyar Afirka wanda ya jefa al'umma miliyan 1.5 dake birnin Goma cikin hadari.

An bayyana cewa wasu alumman yankin da suka kauracewa yankin sun yi hijira zuwa kasar Ruanda makwobciyar kasar mafi kusa.

Mai magana da yawun gwamnatin kasar Patrick Muyaya ya yada a shafukan sadar da zumunta da cewa "Hukumar kasar Na lura da lamarin kain da na in"

An bayyana cewa a shekarar 2002 da Dutsen Nyiragongo mai aman wuta ya fashe ya yi sanadiyar rasa rayukan mutum 250 da kuma rasa gidajen fiye da mutum dubu 120.

 


News Source:   ()