Dubunnan mutane sun yi gudun hijira a Somaliya

Dubunnan mutane sun yi gudun hijira a Somaliya

Sakamakon abubuwan da suka afku a Somaliya a ranar Lahadin nan dubunnan mutane sun yi gudun hijira.

Ofishin Aiyukan Jin Kai na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar da sanarwa ta shafinsa na Twitter cewa, 'yan ta'addar Al-Shabab sun kaiwa jami'an tsaro da fararen hula hari a yankn Mugud da ke tsakiya da arewacin Somaliya.

Sanarwar ta ce, a kalla mutane 31 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin.

Haka zalika an bayyana kashe 'yan ta'addar sama da 40, dubunnan mutanen yankin sun yi gudun hijira.


News Source:   ()