
Wannan dai ita ce zanga-zanga mafi girma a ƙasar cikin shekaru, yayin da ake fama da tsananin talauci.
Tattakin wanda ya yada zango a harabar majalisar dokokin ƙasar, ya samu halartar ‘yan kasuwa, musamman masu sayar da kayan sawa, inda suke kira ga shugaba Lazarus Chakwera da ya yi murabus daga muƙaminsa.
Malawi dai na fama da ƙarancin kuɗaɗen waje, lamarin da ya janyo tashin farashin kayayyakin masarufi da suka haɗa da man fetur da abinci.
Cibiyar Nazarin Manufofin Abinci ta Duniya ta ba da rahoton cewa, a cikin watan Janairu kaɗai, an samu ƙarin kashi 21 na farashin masara, babban abin da ‘yan ƙasar suka fi ta’ammali da shi.
Kusan kashi uku cikin huɗu na al'ummar kasar miliyan 21, na rayuwa cikin matsanancin talauci, yayin da suke fuskantar ƙalubalen tattalin arziki gabanin zabe mai zuwa da za a watan Satumba, inda shugaba Chakwera ke neman wa'adi na biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI