Dubban jama’a sun bar lardin Afar na Habasha saboda Aman wuta na Duwatsu

Dubban jama’a sun bar lardin Afar na Habasha saboda Aman wuta na Duwatsu

Rahotanni sun tabbatar da cewa an fara ganin fashewar duwatsun ne tun a ranar Alhamis ɗin da ta gabata kafin abin ya fara yin ƙamari

An fara kwashe dubban mutanen yankin na Afar dake arewacin ƙasar ta Habasha bayan bindiga da zaɓarɓaka da duwatsun dake aman wuta suka fara yi a dutsen Dofen.

Jama’a sun shiga matsananciyar fargaba dangane da aman wutar da duwatsu ke yi duba da haɗarin da ke tattare da haka.

Aman wutar dutsen na Dofen ta haddasa ɓarna mai yawa a kan gine-gine da hanyoyi tare da lalata kayayyaki a Afar kamar yadda hukumar kare afkuwar bala’ai a lardin ta tabbar.

Wani masanin kimiyya Farfesa Atalay Ayele dake Adis Ababa ya ce aman wutar da dutsen ke yi ba lallai ya hadddasa babbar fashewa.

Dubban jama’a sun yi ƙaura daga lardin Afar na Habasha saboda girgizar ƙasa da Aman wuta na Duwatsu 01:41

Domin nuna wannan labarin, akwai bukatar ka bayar da izinin sanin bayanan masu bibiya da tallace-tallacen kundin adana bayanai na cookies

Amince Zabin son raina Dubban jama’a sun yi ƙaura daga lardin Afar na Habasha saboda girgizar ƙasa da Aman wuta na Duwatsu AP

Yankin Afar na cikin wurare masu zafi gaske dake da tarihin afkuwar girgizar ƙasa da aman wuta na duwatsu.

Ko a wannan lokaci da dutsen na Dofer yay yi aman wutar sai da aka fuskanci girgizar ƙasa da ta kai ƙarfin maki 5.8

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)