Cikin wata sanarwa da kungiyar NRC ta fitar ranar Laraba, ta ce sama da ƴan gudun hijirar Burkina Faso 20,000 da aka yi wa rijista ne ke Zaman mafaka a yankin Koro cercle dake kan iyaka da Burkina tun daga watan Janairun wannan shekara, yayin da wasu da dama da ke dakon a yi musu rajista.
Ƙungiyar ta ce yayin da lokacin bazara ke kara tsananta ƙasar ta Mali, halin da dubban mutanen da suka gujewa tashe-tashen hankula a Burkina Faso don samun mafaka sun kasance cikin yanayin tagayyara.
Ƙasashen biyu na yankin Sahel wanda sojoji ke jagoranta bayan juyin mulki da suka yi, suna fama da tashe-tashen hankula na masu ikirarin jihadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI