Yayin zaman kotun na jiya ne, ta zartas da hukuncin kisan kan Sojojin 13 bayan abin kunyar da suka aikata a yankin Lubero na gabashin lardin Kivu, wanda ta ce ya saɓawa horarwar Soji a ƙasar mai fama da rikicin na tsawon shekaru, ciki har da hare-haren M23 da ke cika shekaru 3 da farowa.
Aƙalla sojoji 24 ne suka gurfana gaban kotu yayin hukuncin na jiya, Baya ga wadanda aka yanke wa hukuncin kisa, hudu sun samu hukuncin zaman shekaru 2-10 a gidan yari, an kuma wanke wasu shida, sannan an ɗage karar daya don ci gaba da bincike.
Yayin da mai gabatar da ƙara a kotun Kabala Kabundi, ya bayyanawa kamfanin dillacin labaru na Reuters cewa an gudanar da shari’ar ce domin tabbatar da ɗorewar ɗa’a da aminci a tsakanin al’umar kasar da kuma dakarun sojin ƙasar
A yayin shari’ar dai dukkanin wadanda aka gurfanar sun amsa laifinsu a yayin da kotun ta baiwa mutum biyar daga cikinsu kwanaki biyar na si ɗaukaka ƙara in sun buƙaci hakan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI