Djibouti ta sanar da nau'in sauron da zai yaƙi mai yaɗa kwayar cuta

Djibouti ta sanar da nau'in sauron da zai yaƙi mai yaɗa kwayar cuta

Ƙasashen gabashin Afrika na ganin ƙaruwar cutar zazzaɓin cizon sauro a baya-bayan nan, sai dai duk da haka Djibouti na cikin ƙasashen da matsalar ke da sauki, inda a bana mutane 27 ne kadai suka kamu da cutar.

Bayanai sun nuna cewa daga shekarar 2012 zuwa yanzu ƙasashen gabashin Afrika sun ga yanayi mai muni a fannin cutar zazzaɓin cizon sauro, lamarin da ya sa ƙasar ta ɗauki wannan mataki.

Masana kiwon lafiya sun ce wannan sabon nau’in sauro na da damar cizon dan adam, kafin yamma likis, lokacin da sauro na gargajiya ya saba fitowa, hakan zai kashe kaifin cutar da ka iya yaduwa a jikin dan adam.

Bayanai sun ce ƙasar Brazil ce ta fara samar da makamancin wannan sauro kuma an gano cewa matakin yayi tasiri kwarai da gaske.

Kawo yanzu ƙasar  ta saki sauron guda 40,000 tun daga watan Mayu zuwa yanzu, kuma ta kuduri sakin adadi mai yawa daga yanzu zuwa watan Afrilun baɗi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)