A cikin wata sanarwa da ta fitar a Litinin, ma’aikatar harkokin wajen Denmark ta ce ta yanke wannan shawarar ce sakamakon juye-juyen mulki har biyu da aka gudanar a ƙasashen, lamarin da ya takaita hulɗa tsakanin su.
Denmark ta ce Tunisia abokiyar hulɗa ce mai mahimmanci a a gem da ƙudirorinta na arewacin Afrika, kuma akwai yiwuwar yauƙaƙa dangantaka ta fannoni kamar sauyin yanayi da sauyawa zuwa makamashi mara illa ga muhalli,a yayin da Senegal kuwa tana da mahimmanci saboda ba ta da tarihin juyin mulkin soji.
Daga cikin wani ɓangare na sabbin dabarunta na mu’ammala da ƙasashen waje, Denmark za ta inganta ofisoshin jakadancinta na ƙasashen Afrika ta Kudu, Kenya, Masar da Nigeria ta inda za su zama cibiyoyi na yankunan da su ke.
Dangantaka tsakanin Burkina Faso da Mali, waɗanda ke yannkin Sahel da wasu ƙasashen yammacin Turai da dama ta yi tsami, tun bayan juyin mulki a ƙasashen a shekarun 2020 da 2022.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI