Tuni ƙasashen suka sanar da ƙirƙiro sabon Fasfo, a maimakon na ECOWAS, to sai dai ofisoshin jakadancin Turai a Bamako sun ƙi bayar da visa ga waɗanda suka gabatar da irin wannan Fasfo
Mutane da dama ciki har da wani tsohon ministan kiwon lafiya na ƙasar ne suka nemi visar Schengen ta hanyar gabatar da wannan Fasfo, amma ofisoshin jakadancin Turai a birnin Bamako suka ƙi bayar da visar.
Lokacin da RFI ta nemi sanin dalilan ƙin bai wa waɗanda ke ɗauke da sabon Fasfo na Mali takardar visa, wasu jami’an diflomasiyyar Turai a birnin Bamako sun ce ba wai ba su amince da shi ba ne, illa kawai an samu sakaci daga da mahukuntan ƙasar Mali, waɗanda ya kamata su gabatar da samfurin wannan Fasfo ga ofisoshin jakadancin Turai don sanar da su a hukumance.
To amma majiyar ta ce matukar aka magance wannan matsala, ba abin da zai hana ƴan Mali samun visar.
Sai dai a cewar ma’aikatar tsaron cikin gidan Mali, kafin ƙaddamar da wannan Passport, sai da aka sanar da illahirin ofisoshin jakadancin Turai da ke ƙasar, tare da tura musu samfuri domin su tabbatar da kamanni da sahihancinsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI