An bayyana cewar daruruwan daliban da 'yan ta'addar Boko Haram suka yi garkuwa da su a makarantarsu da ke garin Kankara na jihar Katsina a arewacin Najeriya, na nan a wani daji da ke jihar Zamfara.
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bayyana cewar sun fara tattaunawa da 'Yan ta'addar don ganin an saki dliban.
Ya ce "Muna tattaunawa ta hanyar jami'an tsaronmu na yanki, amma ba za mu taba yadda mu bayar da kudi ba. A matsayi na na gwamna ni ke da alhakin kubutar da dalibai 402 da aka yi garkuwa da su."
A daren 11 ga Disamba ne 'yan ta'addar Boko Haram suka yi garkuwa da dalibai sama da 500 a makarantar kwana ta sakandire da ke garin Kankara a jihar Katsina.
Bayan kai harin, gwamna Masari ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun jihar.
Ministan Tsaro na Najeriya Bashir Salihi Magashi ya ziyarci yankin tare da yin alkawarin za a kubutar da daliban.