Dakatar da ayyukan agaji da Amurka ta yi, ya yi mumunar tasiri a Congo

Dakatar da ayyukan agaji da Amurka ta yi, ya yi mumunar tasiri a Congo

Jami’in, Bruno Lemarquis ya ce shirin ayyukan jinkai a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ya samu dala biliyan 1 da miliyan ɗari 3, wanda daga cikin adadin, miliyan ɗari 9 da 10 sun fito ne daga Amurka.

Lemarquis ya ce dakatar da ayyukan jinƙai da shugaba Donald Trump ya yi a watan da ya gabata ya sa dole a haƙura da wasu shirye-shirye.

Babban jami’in na Hukumar Agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ya kuma kara da cewa a bisa dole su ka dakatar da ayyukansu a bangarori da dama, la’akari da irin dogaron da  su ka yi a kan tallafin da Amurka ke bayarwa.

Mataki na shugaba Trump na zuwa ne a daidai lokacin da aka shafe gomman shekaru ana fama da matsalar rashin tsaro a gabashin Congo, wanda ya yi sanadiyar jikkata dubban mutane, baya ga saka tsoro a zukatan al’umma na yiwuwar samun barkewar yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)