Dakarun Wagner da na Mali sun aiwatar da hukuncin kisa kan wasu mutane

Dakarun Wagner da na Mali sun aiwatar da hukuncin kisa kan wasu mutane

Wasu majiyoyi da dama a yankin sun tabbatar da cewa aƙalla mutane 6 ne aka aiwatar da hukuncin kisa a kansu a ranar Litinin 2 ga watan Disambar wannan shekara ta 2024 a wannan yanki na Timbuktu, kuma ana ganin adadin na iya ƙaruwa.

Ayarin sojin Wagner da na Mali da ya ƙunshi motoci kimanin 15, sun baro yankin Niafunke a safiyar Litinin ɗin da ta gabata, kuma majiyoyi da dama da tashar Radio france International ta tuntuba, kamar jagororin al’umma da al’ummar yankin Gargando, wasu ƴan tawayen abzinawa daga yankin da kuma ƙwararru masu sanya ido kan tsaro sun ce an aiwatar da hukuncin kisan ne a yankunan Atane da Tignere, a kusa da wata rijiya.

Akasarin waɗanda aka tuntuba sun ce waɗanda aka kashe abzinawa ne makiyaya, waɗanda suka yi turjiya ga sojin mali da mayaƙan Wagner, kuma wata majiyar tsaro a Mali ta tabbatar da hakan, amma ta ce lallai waɗanda aka kashe ƴan ta’adda ne.

Wani faifan bidiyo da sashen faransanci na RFI ya samu, anga harsasai a kawunan waɗanda aka kashe, wasu kuma ɗauke da bandeji, yayin da jama’ar yankin su ka ɓuya cikin daji saboda tsoro da fargaban sojin da suka yi wa yankin nasu ƙawanya a daren Talata.

Har yanzu sojin Mali ba su ce komai ba kan wannan al’amari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)