Bayan bukatar da gwamnatin Libiya ta mika, dakarun sojin Turkiyya sun fara kwance bama-baman da mayakan Haftar suka binne a yankunan da aka fatattake su daga ciki.
An dauki wannan mataki ne domin a kiyaye fararen hula fadawa hatsari a lokacinda suke shirin komawa gidajensu.
Majiyoyin tsaro sun ce, an fara aiyukan kwance bama-baman a Tarabulus Babban birnin Libiya da kuma dukkan gabashin yankin da a baya mayakan Haftar suka mamaye. Domin ba wa fararen hular yankin damar komawa gidajensu cikin lumana, dakarun sojin kasa, sama da na ruwa na Turkiyya sun fara aiyukan tsaftace yankin daga bama-baman da aka binne.
Dakarun na sojin Turkiyya sun saka kayan kariya, suna kuma amfani da mutum-mutumi da fasahar zamani wajen gano bama-baman da mayakan Haftar suka binne tare da kwance su cikin ruwan sanyi.
Gwamnatin Libiya ta bayyana cewar ya zuwa yanzu mutane 27 ne suka rasa rayukansu, wasu 40 suka samu raunuka sakamakon fashewar bama-baman da mayakan Haftar suka binne a unguwannin da suka mamaye a baya amma a yanzu aka kore su daga ciki.