Dakarun Kongo da ke samun goyon bayan sojojin Burundi a ranar Juma'ar nan, sun samu galaba a kan 'yan tawaye masu samun goyan bayan Rwanda a kudancin kasar da ke neman fadada ikonsu a gabashin Kongo a fafatawar da aka shafe makonni ana yi, lamarin da ya haifar da fargabar barkewar wani sabon rikici a yankin.
A farkon makon nan ne 'yan tawayen M23 karkashin jagorancin Tutsi suka kwace birnin Goma, birni mafi girma a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, wanda ke da tarin arzikin zinari, coltan da sauran tarin ma'adanai, kafin su karkata akalarsu zuwa Bukavu da ke makwabtaka da lardin Kivu ta Kudu.
Sai dai bayan wata fafatawa da suak yi, wasu majiyoyi kashi uku ciki har da gwamnan Kivu ta Kudu Jean-Jacques Purusi Sadiki, sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa sojojin Kongo da kawayensu na samun nasarar dakile 'yan tawayen.
Amma Wani shaidan gani da ido ya ce dakaru kusan 1,500 da suka hada da dakarun sojin Kongo da na Burundi da mayakan sa-kai na cikin gida sun samu ci gaba wajen kare garin Nyabibwe mai tazarar kilomita 50 daga birnin Bukavu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI