Dakarun RSF sun sake karɓe iko da babban sansaninsu da ke Darfur

Dakarun RSF sun sake karɓe iko da babban sansaninsu da ke Darfur

Rikici tsakanin dakarun RSF da sojojin Sudan ya ɓarke ne tun a cikin watan Afrilun 2023 kuma ɓangarorin biyu sun gwabza wasu daga cikin mummunan faɗace-faɗace a yankin Arewacin Darfur saboda yadda kowanne daga cikinsu ke ƙoƙarin mallakar tungar ƙarshe a yankin.

Tun a ranar Asabar dakarun haɗaka da sojin Sudan suka fitar da wata sanarwa wadda ta ce, sun karɓe iko da sansanin na al-Zurug, sansanin da RSF ke amfani da shi tun bayan ɓarkewar yakin Sudan watanni 20 da suka gabata.

Daga wannan sansanin ne, RSF ke jigilar wasu kayayyakin buƙatun yau da kullum zuwa kan iyakokin Chadi da Libya.

An dai kashe gwamman dakarun na RSF tare da kona motocinsu, yayin da kuma aka kwace kayayyakin da suke jigilar su a yayin farmakin.

Bayan kaddamar da harin, RSF ta zargi dakarun haɗakar da kashe hatta fararen hula da suka haɗa da mata da ƙananan yara tare da kona gidajensu har ma da kayayyakin more rayuwa na talakawa  baya ga kasuwanni da rijiyoyi da makarantu da asibitoci da suka banka wa wuta.

Koda yake ita ma rundunar haɗakar ta zargi RSF da yin amfani da wannan sansani wajen kai wa fararen hula munanen hare-hare.

Sai dai yanzu RSF ɗin ta yi kukan kura tare da sake ƙarbo sansanin nata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)