"Mutane 13 ne suka mutu sakamakon harbin da RSF ta yi kan fararen hula a garin Al-Hilaliya, a gabashin jihar Al-Jazeera, mai tazarar kilomita 70 daga arewacin Wad Madani, babban birnin jihar," in ji majiyar likitocin.
Sudan ta fada cikin rikici tun a watan Afrilun 2023, bayan wani yaki da dakarun FSR karkashin jagorancin Janar Mohamed Hamdane Daglo suka yi da sojoji, karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhane, shugaban kasar.
Birnin Khartoum na kasar Sudan © Rashed Ahmed / APA halin yanzu dai mayakan na ci gaba da gwabza kazamin fada a jihar Al-Jazeera da ke karkashin ikon RSF tun karshen shekarar da ta gabata.
Bayan sauya sheka da daya daga cikin shugabanninsu na wannan jiha ya yi ya shiga sansanin ‘yan adawa, ‘yan ta’addan sun kaddamar da hare-hare a wasu yankuna tare da yin arangama, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 200 a cikin kwanaki goma kamar yadda hukumomi da likitoci suka bayyana.
Wasu daga cikin yankunan da dakarun RSF suka kai hari REUTERS - StaffGuguwar tashe-tashen hankula a jihar Aljazeera ya yi sanadiyar raba mutane kusan 119,000 zuwa jihohin Kassala da Gedaref, a cewar ofishin kula da jin kai na Majalisar Dimkin Duniya na Ocha.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI