Dakarun Libiya sun kwace sansanin Watiyya

Dakarun Libiya sun kwace sansanin Watiyya

Dakarun gwamnatin Libiya sun kai hare-hare ta sama sau 5 a cikin awanni 24 da suka gabata kan mayakan dan tawaye Haftar da ke sansanin sojin sama na Watiyya a gabashin Tarabulus Babban Birnin Kasar.

A hare-haren ta sama an lalata motocin yaki da kayan aiki mallakar 'yan tawayen mabiya Haftar inda aka kuma kassara 7 daga cikinsu.

A ranar 25 ga watan Maris ne gwamnatin Libiya da kasashen duniya suka amince da ita ta fara kai 'Farmakan Guguwa', a ranar 13 ga Afrilu ta fatattaki 'yan ta'adda daga yammacin Tarabulus a wasu unguwanni 7 inda sai da ta dangana ga iyakar kasar da Tunisiya.

Sansanin Watiyya da ke tsakiyar Sahara na da matukar muhimmanci saboda yadda yake iya daukar sojoji dubu 7 zuwa 10 a lokaci guda.

Sojojin Libiya sun kuma bayyana cewar sun samu nasarar kwace sansanin da ake amfani da shi wajen kai wa fararen hula hare-hare a Tarabulus.


News Source:   www.trt.net.tr