Dakarun Afrika ta Tsakiya sun kubutar da birnin Bouar daga hannun 'yan tawaye

Dakarun Afrika ta Tsakiya sun kubutar da birnin Bouar daga hannun 'yan tawaye

Jami'an tsaron Jamhoriyar Afirka ta Tsakiya sun yi nasarar kubutar da birnin Bouar da ya kasance hannun 'yan tawaye na tsawon kwanaki 25.

Kamar yadda hukumar ta sanar da taimakon sojojin Rasha da na Ruwanda jami'an tsaron kasar sun yi nasarar kubutar da birnin Bouar mai muhinmanci da 'yan tawayen suka karbe a 'yan makonnin da suka gabata.

A rikicin da ya barke tsakanin jami'an tsaro da 'yan tawayen ne a tsakanin ranakun 9-17 ga watan Janairu da yawan al'umman birnin suka fice daga matsuguninsu damar da 'yan tawajen suka samu na karbe ikon birnin.

A kasar da kaso 80 cikin darin kasar ke hannun 'yan bindiga jami'an tsaron kasar na kokarin kubutar da muhinman birane inda suka kubutar da biranen Boali, Bossembele da Yaloke daga bisani kuma suka karbe birnin Bouar daga hannun 'yan tawayen.

 


News Source:   ()