Dakarun AES dubu 5 na gab da fara aikin yaƙi da ta'addanci a Sahel

Dakarun AES dubu 5 na gab da fara aikin yaƙi da ta'addanci a Sahel

Wani jawabin kai tsaye da ministan tsaron Nijar Salifou Mody ya gabatar ta gidan talabijin ne ke sanar da wannan shiri wanda ya ce nan ba da jimawa ba, ƙasashen 3 za su girke wannan dakaru.

Ƙasashen 3 na yankin yammacin Afrika da dukkaninsu ke ƙarƙashin mulkin Sojoji da suka kifar fa gwamnatocin fararen hula a shekarun 2020 da 2023 sun amince da haɗa ƙarfi don yaƙar matsalolin tsaron da suka dabaibayesu bayan yanke alaƙa da uwar goyonsu Faransa.

A cewar ministan tsaron, haɗakar dakarun wadda za a yiwa suna da dakarun AES za a wadata da dukkanin kayakin buƙatar soji kama daga makamai da sassan bincike da tattara bayanan sirri ta yadda za ta riƙa gudanar da ayyukanta a tsakanin ƙasashen don kawar da barazanar tsaro.

Ministan tsaron na Nijar Salifou Mody ya bayyana cewa aikin samar da dakarun aƙalla dubu 5 da kuma rarrabasu ya kankama ta yadda ya rage lokaci ƙanƙani a fara ganin aikinsu a zahiri.

Ƙasashen 3 waɗanda suka fice daga haɗakar ECOWAS na ƙoƙarin magance matsalolin tsaron da suka dabaibayesu ne bayan fantsamuwar ƙungiyoyin ƴan ta’adda masu alaƙa da Al Qaeda.

Zuwa yanzu akwai mutane aƙalla miliyan 2 da dubu 600 da rikicin ya raba da matsugunansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)