Dakaraun sa kai na RSF a Sudan sun kashe mutane 12

Dakaraun sa kai na RSF a Sudan sun kashe mutane 12

Wani rahoto na bayyana cewa "farar hula 12 ne suka mutu yayin da wasu biyar suka jikkata a harin da RSF ta kai a yau" a arewacin garin Kutum da ke arewacin Darfur.

Kwamitin Resistance Local, wata kungiya mai fafutukar tabbatar da dimokuradiyya da ke shirya taimakon juna tsakanin mazauna yankin ta karasa da cewa harin ya yi muni ,ta kuma  yi tir da "kisan gilla", ta kara da cewa dakarun yan sa kai na RSF sun kama mutane uku ciki har da likita.

Wasu daga cikin mutanen da rikicin Sudan ya raba da muhallensu Wasu daga cikin mutanen da rikicin Sudan ya raba da muhallensu REUTERS - Thomas Mukoya

Dakarun RSF sun kona kauyuka kusan ashirin a yankin guda, inda suka yi tir da gwamnan yankin na Darfur, Minni Arcou Minnawi, wanda tsohon madugun 'yan tawaye ne a yanzu da ke kusa da sojoji.

Sudan ta fada cikin rikici tun a watan Afrilun 2023 sakamakon yakin da ake yi tsakanin kungiyar RSF karkashin jagorancin Janar Mohamed Hamdane Daglo da sojoji karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhane, shugaban kasar.

Kasar Sudan Kasar Sudan © Marwan Ali / AP

Yakin na Sudan ya yi sanadin mutuwar dubun-dubatar mutane, inda aka yi kiyasin daga 20,000 zuwa 150,000, inda akasarin wadanda abin ya shafa ya raba miliyoyin mutane da muhallansu tare da haifar da daya daga cikin mafi munin rikicin jin kai a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)