Mutane 11 sun dake rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar shawara a Najeriya wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa 76.
Shugaban Hukumar Kula da Cututtuka ta Najeriya Chikwe Ihekweazu ya shaida cewar an samu bullar cutar a jihohin Enugu, Delta da Bauchi.
Ihekweazu ya shaida cewar a tsakanin 1 da 11 ga Nuwamba mutane 222 ne suka kamu da cutar a jihohin 3, kuma 76 daga ciki sun rasa rayukansu.
Ya ce, sun fara daukar matakan yaki da cutar a fadin kasar.
A shekarar da ta gabata, mutane sama da 300 cutar zazzabin shawara ta kashe a Najeriya.