Cutar shan inna mai nakasa kananan yara ta sake bulla a kasar Kamaru.
Ma'aikatar Lafiya ta Kamaru ta ce, cutar ta sake bulla inda ta kama mutum 1 a Yaounde Babban Birnin kasar.
Sanarwar ta ce, akwai yiwuwar cutar ta yadu cikin sauri, kuma an fara daukar matakan hana ta yaduwa, haka zalika an bayyana bukatar fara gangamin yin allurar riga-kafin cutar.
Bayan da aka dauki lokaci tun daga 2015 har zuwa shekarar da ta gabata ba a samu bullar cutar a Kamaru ba, a ranar 18 ga Yunin 2020 Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya ta aiyana cewa babu sauran cutar shan inna a kasar da ta dade tana yaki da ita.
Cutar shan inna na kama yara 'yan shekaru 5 zuwa kasa.
Cutar shan inna na nakasa yaro 1 daga cikin 200 da ta kama wanda kuma ba ya komawa daidai a rayuwarsa.
Haka zalika kaso 5 zuwa 10 na wadanda cutar ke kamawa suna mutuwa bayan illata gabobinsu da cutar ke yi.
Cutar shan inna da ta ke da nau'ika 3 na Tip 1, Tip 2 da Tip 3 na rayuwa a wajen jikin dan adam na tsawon lokaci.
Cutar ba ta da wani takamaiman magani, amma tana da allurar riga-kafi mai tasiri.