A kasar Gambiya da ke yammacin Afirka an samu bullar cutar shan inna.
Ministan Lafiya na Gambiya Ahmadou Lamin Samateh ya shaida cewa, a samfuran da aka dauka a jikin yara kanana a Banjui Babban Birnin kasar da yankin Kotu na gabar teku an gano cutar shan inna da aka fi sani da Polio.
Samateh ya ce, wannan cuta mai ban tsoro na yawo a cikin kasar da ke da mutane miliyan 2, kuma gwamnati ta fara shirin gudanar da gangamin hana cutar yaduwa.
Samateh ya kara da cewa, gangamin ya shafi yara kanana masu shekaru 5 zuwa kasa.
Baya ga Gambiya, a kasashen Afirka da suka hada da Uganda, Benin, Burkina Faso, Kamaru, Itopiya, Mali, Nijar, Chadi da Sudan an samu bullar cutar ta shan inna.