Cutar kwalara ta yi ajalin mutane dubu 2,141 a Najeriya

Cutar kwalara ta yi ajalin mutane dubu 2,141 a Najeriya

Adadin mutanen da cutar kwalara ta yi ajali a Najeriya ya karu zuwa dubu 2,141.

Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) na cewa, a tsakanin 1 ga Janairu da 3 ga Satumaba cutar ta yadu a jihohin Najeriya 23 da Abuja Babban Birnin Kasar.

Mutane dubu 65,145 cutar ta kama a wannan lokaci inda ta yi ajalin dubu 2,141.

A jihar Kano aka fi samun kamuwa da cutar da mutane dubu 10,343 inda jihar Katsina kuma ta fi samun rasa rayuka da mutuwar mutane 150.

Daraktan NCDC Dr. Chikwe Ihekwezu ya shaida cewa, kasp 26 na wadanda suka kamu da cutar masu shekaru 5 zuwa 14 ne.

Ihekweazu ya kara da cewa, sun fara gangamin yaki da yaduwar cutar a Najeriya, ya kuma bukaci jama'a da su baiwa tsafta muhimmanci.

Shan ruwa ko abinci da ke dauke da kwayoyin cuta na "VibrioCholerae" ne ke janyo kamuwa da cutar. Tana janyo amai da gudawa da rasa ruwan jiki wanda idan ba a dauki matakin magani da wuri ta ke yin ajalin wadanda suka kamu.


News Source:   ()