A mako dayan da ya gabata cutar kwalara ta yi ajalin mutane 63 a Najeriya.
Cibiyar Yaki da Cuttuka ta Najeriya ta fitar da rahotonta na mako-mako inda cutar ta ke ci gaba da yaduwa a sauran jihohi, kuma ta kama mutane dubu 3,098 a mako dayan da ya gabata.
Tun daga watan Janairu zuwa yau mutane dubu 58,690 cutar kwalara ta kama a Najeriya, ta kuma yi ajalin wasu kusan dubu 2.
Shan ruwa ko abinci da ke dauke da kwayoyin cuta na "VibrioCholerae" ne ke janyo kamuwa da cutar. Tana janyo amai da gudawa da rasa ruwan jiki wanda idan ba a dauki matakin magani da wuri ta ke yin ajalin wadanda suka kamu.