Cutar kwalara ta yi ajalin mutane 60 a Najeriya

Cutar kwalara ta yi ajalin mutane 60 a Najeriya

Mutane 60 sun rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar kwalara a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya.

Daga watan Janairu zuwa yanzu sama da mutane 500 cutar kwalara ta kashe a fadin Najeriya.

Kwamishinan Lafiya na jihar Katsina Yakubu Danja a yayin taron manema labarai na Kungiyar Likitoci ta Najeriya ya shaida cewa, annobar kwalara ta fara yiwa jihar barazana.

Danja ya ce, "A yanzu akwai mutane dubu 1,400 da aka samu dauke da cutar kwalara a jihar Katsina. Ya bukaci mazauna jihar da su dauki matakan kariya."

 


News Source:   ()