Cutar kwalara ta yi ajalin mutane 325 a Najeriya

Cutar kwalara ta yi ajalin mutane 325 a Najeriya

Tun daga watan Janairu zuwa yau mutane 325 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar kwalara a Najeriya.

Daraktan Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Najeriya Dakta Chikwe Ihekweazu ya shaida cewa, daga watan Janairu zuwa yau cutar kwalara ta yadu a jihohi 15 da suka hada da Kano, Plateau da kuma Abuja Babban Birnin Kasar.

Ihekweazu ya shaida cewa, a wannan lokaci jimillar mutane 325 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar ta kwalara.

Jami'in ya kuma ce, ya zuwa yanzu kwalara ta kama mutane dubu 15,343inda mafi yawansu suke tsakanin shekaru 4 da 15.

Ya kara da cewa, gwamnati ta dauki matakan kariya yadda ta kamata inda ya yi kira ga jama'a da su dauki karin matakan tsafta.


News Source:   ()