Mutane 20 sun rasa rayukansu sakamakon barkewar annobar kwalara a jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya.
Kwamishinan Lafiya na jihar Bauchi Dakta Aliyu Migoro ya sanar da cewa, an samu mutane 322 a yankunan jihar daban-daban dauke da cutar ta kwalara.
Maigoro ya ce, 20 daga cikin mutanen da cutar ta kama sun rasa rayukansu, an kuma kai wasu da dama zuwa asibiti.
Ya bayyana an kai magunguna da kayan kula da lafiya zuwa yankunan da cutar ta bulla.
Maigoro ya yi kira ga jama'ar yankunan da su dauki matakan kariya daga cutar, kuma da zarar sun ga wani da ake tunanin na dauke da cutar to a sanar da mahukunta.
Sakamakon rashin samun tsaftataccen ruwan sha da kula da lafiya cikin sauri a Najeriya ya sanya cutar kwalara ke kama mutane tare da yin ajalinsu cikin sauri.