Cutar HIV ta yi sanadiyar rayuka miliyan 1.6 a Najeriya

Cutar HIV ta yi sanadiyar rayuka miliyan 1.6 a Najeriya

Masana sun sanar da cewa cutar HIV mai karya garkuwar dan adam ta yi sanadiyar rayuka miliyan 1.6 a kasar Najeriya dake yammacin Afirka. 

Cibiyar dake kula da masu dauke da cutar HlV da aka fi sani da kanjamau ta gudanar da taro a ranar HIV ta duniya ta 1 ga watan Disamba a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya. 

A taron wakilin Hukumar Aiki Akan Cutar HIV ta Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya Dkt. Erasmus Morah ya bayyana cewa kawo yanzu a Najeriya cutar HlV tayi sanadiyar rayuka miliyan 1.6.

Morah dake bayyana cewa masu dauke da cutar HlV na fuskantar muamala mara kyau ya kara da cewa shirye suke su bayar da taimako domin yakar cutar. 

A gefe guda kuma jami'i daga Hukumar Yaki da cutar HlV a Najeriya Dkt Gambo Aliyu ya bayyana cewa ya zama wajibi a rinka yin gwajin cutar domin ita ce hanya tilo da za a iya magance cutar cikin sauki. 


News Source:   ()