Ma'aikatar Lafiya ta Gini ta bayyana cewar, cutar Ebola ta sake bulla a garin Goueke na kudu maso-yammacin kasar.
An bayyana cewar, daga shekarar 2016 zuwa yau, a karon farko mutane 4 sun rasa rayukansu sakamakon cutar Ebola akasar.
Ma'aikatar ta ce "Idan aka kalli dokokin kasa da kasa na kula da lafiya, gwamnatin Gini ta aiyana dokar ta baci a garuruwan Goueke da Nzerekore sakamakon bullar cutar Ebola."
A garin Goueke an kebe dukkan wadanda suka kamu da cutar da wadanda suka yi mu'amala da masu dauke da ita, kuma za a samar da wata cibiya don kula da su, sannan za a hanzarta kawo allurai ta hanyar hada kai da Hukumar Lafiya ta Duniya.
A tsakanin shekarun 2013-2016 annobar Ebola ta yi ajalin akalla mutane dubu 11,300 a kasashen Afirka da suka hada da Gini, Laberiya da Saliyo.