Wata cuta da har yanzu ba a iya gano wacce iri ba ce, na ci gaba da yin ajalin mutane a arewacin Najeriya.
A jihar Jigawa da ke arewa maso-yammacin Najeriya mutane sama da 100 ne suka mutu a cikin kwanaki 10 da suka gabata sakamkon kamuwa da ciwon da ba a san wanne iri ba ne.
Kwamishinan Lafiya na jihar Dr. Abba Zakari ya shaida cewar kwararru daga Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) sun isa j,har don gudanar da binciken gano wacce irin cuta ce ta ke yin kisan.
Ya ce "Ya yi wuri idan aka ce cutar Corona ce ko kuwa ba ita ba ce, amma kwararru sun fara bincike."
A jihar Kano ma da ke arewacin Najeriyar, a watan da ya gabata mutane sama da 150 sun mutu a cikin kwanaki 3.