Cutar amai da gudawa ta yi ajalin mutane 25 a Najeriya

Mutane 25 sun rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar amai da gudawa a jihohin Benue da Oyo da ke Najeriya.

Labaran da jaridun kasar suka fitar sun rawaito Kwamishinan Lafiya na jihar Benue Dr. Emmanuel Ikwulono na cewa a yankin Okpeilo-Otukpa mutane 17 sun mutu sakamakon kamuwa da cutar amai da gudawa.

Ya ce, an kwantar da wani mutum a asibiti sakamakon kamuwa da cutar, kuma jama'ar yankunan sun firgita.

Sanarwar da wani jami'in Hukumar Kula da Lafiya ta jihar Oyo ya fitar ta ce, mutane 8 sun mutu a yankin Lagelu na Ibadan sakamakon kamuwa da cutar amai da gudawa, an kwantar da wasu 10 a asibiti.

Jami'in ya kuma ce an fara daukar matakan hana cutar yaduwa zuwa jihohi makota.


News Source:   ()