Mutane 24 sun rasa rayukansu sakamakon bullar cutar amai da gudawa (kwalara) a jihar Bayelsa da ke kudu maso-kudancin Najeriya.
Labaran da jaridun Najeriya suka fitar sun rawaito kwamishinan lafiya na jihar Bayelsa Dr. Pabara Newton-Igwele na cewa, an kai magunguna da kayan bayar da agajin gaggawa zuwa yankunan da cutar ta bulla.
Newton-Igwele ya yi kira ga jama'ar yankin da su dauki matakan kariya daga cutar, kuma su bayar da labari ga mahukunta da zarar sun ga wani dauke da ita.
Sakamakon rashin samun tsaftataccen ruwan sha a Najeriya, ana yawan kamuwa da cutar amai da gudawa.