A baya ma kungiyoyin bada agaji sun yi irin wannan gargadi kamar wata guda da ya gabata bayan gano yadda cutar ke nuna alamar yin barazana ga al’umma.
A cewar rahoton dai zuwa ranar Jumma’ar da ta gaba ta akalla mutane 737 ne suka kamu da cutar amai da Gudawa a baban birmin kasar wato Malakal .
Bisa ga dukkan alamu dai al’amarin sai kara hayayyafa yake yi, musamman ma a babban birnin kasar .
Sauran garuruwan da annobar ta fi shafa dai sun hada da Tonga da kuma Kodak a cewar Zakariya Mwatiya, jagorar kungiyoyin agaji a Sudan ta Kudu.
Ya kara da cewa ana samun sauki idan a ka sami kulawar gaggawa amma kuma cutar na da saurin kisa cikin yan sa’o’I idan ba’a sami kulawa nan take ba.
A garin Malakal kada,i an kwantar da mutane 100 a asibiti sai dai kuma ana fama da karacin ruwa da tsafaceccen muhalli ga kuma karancin masu bada agaji.
A farkon wannan watan mutane 1, 526 su ka kamu da cutar kuma akalla yan gudun hijra 850,000 su ka yi kaura daga Sudan zuwa Sudan ta Kudu cikin watanni 18, lamarin da ka iya ta’azzara matsala a kasar da ke fiskantar kalu bale.
Tuni majalisar Dinkin Duniya ta bada gudumowar allurar rigakafi 280,000 dan rarrabawa .
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI