A shekarar 2019 da ta gabata yara kanana dubu 22,000 ne suka kamu da Cuta Mai Karya Garkuwar Jiki a Najeriya.
Rahoton da aka fitar daga Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) game da Ranar cutar Kanjamau ta Duniya ta bayyana cewar, a 2019 yara kanana masu shekaru 0 zuwa 14 dubu 22 ne suka kamu da cutar a Najeriya.
Rahoton ya ce, a yanzu a Najeriya akwai yara kananan dubu 150 da ke dauke da cutar HIV, kuma wannan abu ne mai rikita kwakwalwa da tunani.
Haka zalika rahoton ya kara da cewar, a shekarar da ta gabata yara kanana dubu 110 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Kanjamau, kuma dubu 13 daga ciki suna Najeriya.
Rahoton ya kara da cewar, akwai karancin kayan aikin kare yara kanana daga kamuwa da cutar ta HIV a Najeriya, kuma duk kokarin da ake yi amma lamarin na kara munana a tsakanin yara kanana.