Corona ta yi ajalin mutum 833 a Najeriya

Corona ta yi ajalin mutum 833 a Najeriya

A ‘yan kwanakin da suka gabata anga karin yawan kamuwa da kwayar cutar Corona a kasar Najeriya inda a cikin awannin da suka gabata an samu mutum 640 dauke da cutar da kuma mutuwar karin mutum 20 sanadiyarta.

Yawan wadanda cutar ta yi ajali sun kai 833 inda yawan wadanda suka kamu da cutar a kasar ya haura dubu 38,948.

Zuwa ranar Alhamis mutum dubu 16,061 sun warke an kuma sallamesu daga asibiti kamar yadda Hukumar Kare Yaduwar Cututtuka ta Kasar (NCDC) ta sanar.

Babban birnin kasuwancin kasar Lagos, babban birnin tarayyar kasar Abuja da jihar Oyo dake kudu maso yammacin kasar ne suka fi fuskantar kalubalen kwayar cutar ta Covid-19 a Najeria.

 

 

 

 

 

 


News Source:   ()