A kasar Saliyo da ke Yammacin Afirka an sake saka dokar hana fita waje sakamakon annobar Corona (Covid-19).
Shugaban Kasar Saliyo Julius Maada Bio ya sanar da cewa, a karkashin matakan yaki da yaduwar cutar da ake samu a kasar, an saka dokar hana fita ta kwanaki 30.
Shugaban ya ce, an saka dokar hana fita waje daga karfe 21.00-05.00 inda ba a yarda sama da mutane 50 su taru a waje guda a lokaci daya ba.
Bio ya kara da cewa, daga ranar Juma'ar da ta gabata za a rufe dukkan wuraren ibada, sannan za a rufe gidajen giya da na sayar da abinci da wuri.
A Saliyo da ke da yawan mutane miliyan 7,5 ya zuwa yau jimillar mutane dubu 5,652 cutar Corona ta kama inda dubu 3,586 suka warke, wasu 102 kuma suka rasa rayukansu.