Jamhuriyar Afirka ta Kudu ta karbi kashin farko na allurar riga-kafin Corona (Covid-19) ta BioNTech/Pfizer.
Ministan Lafiya na Afirka ta Kudu Zweli Mkhize a shafinsa na Twitter ya yada hotunan jirgin dakon kaya da ya sauke kayan a filin tashi da saukar jiragen sama na OR Tambo.
Nan da watan Yuni kasar za ta karbi allurar riga-kafin Pfizer miliyan 4,5.
Sakamakon yadda allurar AstraZeneca ba ta bayar da garkuwa ga sabon nau'in Corona ya sanya Afirka ta Kudu ajje ta tare da fara amfani da ta kamfanin Johnson&Johnson na Amurka.