Cikin watan jiya ne hukumar lafiya ta duniya WHO ta ayyana dokar ta ɓaci kan cutar ta ƙyandar biri lamarin da ya ja hankalin duniya wajen ɗaukar matakan yaƙi da cutar, sai dai har zuwa yanzu babu allurar rigakafi ko guda ɗaya da ta isa Congo duk da cewa ƙasar ta fi kowacce galabaituwa daga cutar.
Shugaban sashen yaƙi da cutar tan ƙyandar biri a Congo Cris Kacita ya shaidawa Reuters cewa kowanne lokaci a yau Alhamis ne ƙasar ke sa ran karɓar rukunin farko na alluran yayinda za ta karɓi rukuni na biyu a ranar Asabar 7 ga wata.
Jami’in wanda bai bayyana adadin alluran da za su isa ƙasar ba, ya ce a kowacce rana ana ganin sabbin kamuwa da cutar ta ƙyandar biri a sassan Congo.
Da safiyar yau Alhamis shugaban hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya tabbatar da cewa alluran na gab da isa Congo kowanne lokaci daga yanzu don ɗaura azamar kawar da cutar.
A cewar WHO an samu alluran ne daga kamfanin harhaɗa magunguna na Bavarian Nordic wanda ya samar da su bisa tallafin ƙungiyar tarayyar Turai.
Tun gabanin wannan yunƙuri tuni haɗakar Gavi da ke samar da alluran rigakafi ta bayyana cewa rukunin farko na rigakafin da zai isa Congo na ɗauke da allurai dubu 200.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI