Congo: 'Yan tawayen M23 sun karɓe iko da birnin Goma

Congo: 'Yan tawayen M23 sun karɓe iko da birnin Goma

Da sanyin safiyar wannan Litinin ce mazauna Goma suka wayi gari da jiyo rugugin manyan bindigogin da ake musayar wuta dasu, daga bisani kuma ‘yan tawayen na M23 suka sanar da kame birnin, tare da bai wa sojojin Jamhuriyar Congo wa’adin awanni 48 da su taru a babban filin wasa dake birnin na Goma don mika wuya da ajiye makamansu.

Sai dai duk da cewa ‘yan tawayen na M23 sun bukaci mazauna birnin mai cike da arziki da su kwantar da hankulansu, akwai alamun tsananin firgici a tsakanin jama’a, la’akari da yadda hotunan bidiyo na farko da suka fara fita da safiyyar ta wannan Litinin, suka nuna yadda titunan birnin na Goma suka kasance babu kowa tamkar an yi ruwa an ɗauke.

Kufcewar birnin Goma daga hannun gwamnatin Congo na zuwa ne sa’o’i bayan da mahukuntan ƙasar suka katse duk wata laƙa da Rwanda, wadda ke cigaba da musanta zargin da ake mata na goyon bayan ‘yan tawayen M23, duk da cewar hujjojin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta tattara sun tabbatar da zargin.

Tasirin rikicin da kuma illarsa

 

Akwai fargabar cewa hare-haren da ‘yan tawayen M23 ke cigaba da kai wa ka iya sake ƙazanata ɗaya daga cikin yaƙe-yaƙe mafiya daɗewa a nahiyar Afirka ta hanyar tagayyara fararen hular da ke rasa gidajensu.

A wani rahoto da ta walllafa a baya bayan nan,  Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce a halin da ake ciki, fiye da 1 bisa 3 yawan al’ummmar lardin Arewacin Kivu inda birnin Goma yake, sun zama ‘yan gudun hijira saboda kazamin faɗan da aka jima ana yi tsakanin dakarun Congon da mayakan M23, kuma kame birnin da ‘yan tawayen suka yi zai sake ta’zzara mummnan yanayin da ake ciki na fama da laifukan take hakkin ɗan Adam da suka haɗa yawaitar yi wa mata fyaɗe, azabtarwa, da kuma kisan gilla.

Ko da yammacin ranar Lahadi wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Congo ya shaidawa Kwamitin Tsaro cewar, al’ummmar arewacin Kivu musamman na birnin Goma na cikin tsaka mai wuya, domin yanzu haka ilharihin filayen jiragen sama da hanyoyin kan tudu duk a rufe suke, lamarin da ya katse duk wani aiki na jin ƙai.

Tushen wannan tashin hankali dai shi ne rikicin kabilanci da yayi muni tsakanin ‘yan ƙabilun Hutu masu kusanci da gwamnati Jamhuriyar Congo da kuma kungiyoyin mayaƙan Tusti da wasu tsirarun kabilu da ake zargin suna samun goyon bayan kasashen Uganda da Rwanda. Kodayake ƙasashen sun sha musanta zargin da ake musu na taimakawa mayaƙan na M23.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)