Congo ta yanke hulɗar jakadanci da Rwanda saboda rikicin ƴan tawayen M23

Congo ta yanke hulɗar jakadanci da Rwanda saboda rikicin ƴan tawayen M23

Ayyukan ƙungiyar ƴan tawayen ta M23 da ta shafe shekaru 3 tana aiwatarwa, sun tsananta a yankin gabashin Congo mai ɗinbin arziƙin albarkatun ƙasa, baya ga kwace iko da manyan birane, wanda hakan ya tilastawa Majalisar Ɗinkin Duniya yin gargaɗin kan yiwuwar tsanantar yaƙi a yankin.

Sojin Congo da dakarun wanzar da zaman lafiya na ƙoƙarin dakatar da ƴan tawayen daga mamaye yankin yammacin Goma, babban birnin arewacin Kivu.

Ƙungiyar tawayen M23 dai ƙungiyar dakaru ne da suka balle daga cikin na Congo sama da shekaru 10 da suka gabata, tun dawowar ta a shekarar 2022 ta ke ƙara tasiri tare da mamaya a gabashin Congo.

Congo da Majalisar Ɗinkin Duniya sun zargi Rwanda da tallafawa M23 da dakaru haɗi da makamai, wanda ƙasar ta sha musawa.

Kakakin rundunar tsaron Congo, Janar Sylvain Ekenge ya bayyana cewa sojinsu na aiki don yaƙi da maƙiya, yayin da Rwanda ta duƙufa domin kwace birnin Goma.

Ƙasashen Amurka, Birtaniya da Faransa sun umarci al’ummarsu mazauna Congo su fice daga Goma tun filayen jiragen sama da iyakoki na buɗe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)