Wannan matakin na cikin wani shiri ne na rage cinkoso a gidajen yarin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo wanda ke gudana a ƙarƙashin jagorancin Ministan Shari’a na Ƙasar.
Kimanin fursunoni dubu 15 ake garkame da su a gidan yarin na Makala, adadin da ya ruɓanya har sau goma bisa ainihin yawan fursunonin da gidan yarin ya kamata ya ɗauka a lokaci guda.
Bayanai na cewa, halin da waɗannan fursunoni ke ciki na tayar da hankali, yayin da a farkon wannan watan na Satumba aka samu asarar mutane 150 daga cikinsu.
Yanzu haka fursunonin da aka sake su sun fara samun kulawar likitoci a asibiti bayan Ma’aikatar Shari’ar Ƙasar ta kwaso su a cikin motocin bas-bas.
Tuni Ministan Shari’ar, Constant Mutamba ya yi tur da yadda aka gaza kula da fursunoni marasa lafiya a gidan yarin, sannan ya bada umarnin yi wa gidan yarin feshin maganin kashe kwayoyin cuta da kuma samar musu da magunguna.
Sai dai tuni masharta suka ɗiga ayar tambaya kan ingaancin wannan shirin na rage cinkoson fursunonin, ganin yadda ake ci gaba da kawo sabbin masu laifi ana garkame su bayan kwashe marasa lafiyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI