Congo ta nemi agajin Sojoji daga Chadi don murƙushe mayaƙan M23

Congo ta nemi agajin Sojoji daga Chadi don murƙushe mayaƙan M23

Shugaba Felix Tshiesekedi na Congo a wani saƙo da ya aika zuwa Chadin ta hannun jakada na musamman Didier Mazenga a Talatar da ta gabata ya roƙi shugaba Mahamat Idriss Deby da ya taimakawa Kinshasa a matsalolin tsaron da suka dabaibayeta.

Kafar yaɗa labarai ta RFI ta ruwaito jakadan na isar da wannan saƙon Tshiesekedi ga Deby cike da fatan samun tallafi don fatattakar mayaƙan na M23 masu samun goyon bayan Rwanda.

Rahotanni sun ce an yi doguwar tattawanawa tsakanin Didier Mazenga da shugaba Mahamat Deby kodayake babu tabbacin irin batutuwan da suka tattaunawa da kuma matsayar da suka cimma.

Zuwa yanzu M23 ta ƙwace kusan dukkanin lardin Kivu bayan kame biranen Goma da Bukavu, duk kuwa da yadda taron ƙungiyar AU ya yi doguwar tattaunawa a ƙoƙarin laluben hanyoyin warware rikicin ƙasar.

A farkon watan nan ne, shugaba Deby na Chadi ya fito ya bayyana cikakken goyon baya ga Congo tare da nanata buƙatar girmama ta a matsayin ƙasa mai cikakken iko da dukkanin yankunanta saɓanin katsalandan ɗin da Rwanda ke mata.

Aƙalla mutane miliyan 7 ko fiye ne yanzu haka ke gudun hijira a sassan Congo bayan tsanantar rikicin da ƙasar ke fama da shi na fiye da shekaru 20 ko da ya ke mamayar M23 a yanzu ita tafi ta’azzara lamurra.

Daga watan Janairun shekarar nan kawo yanzu M23 ta hallaka mutane fiye da dubu 3 bayan jikkata wasu dubbai da kuma tilastawa mutum fiye da dubu 500 barin matsugunansu.

A gefe guda ƙungiyar mai samun goyon bayan Rwanda ta kuma hallaka jami’an wanzar da zaman lafiya 20 ciki har da sojojin Afrika ta kudu 14.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)