Shi dai Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya na da kujerun mambobi 5 na dindindin, da suka hada da China da Faransa da Rasha da Birtaniya da kuma Amurka, sannan akwai kujeru 10 na mambobin da ke zaɓa duk bayan shekaru biyu, sai dai basu da ikon hawa kujerar naƙi gama da ɗaukar mataki.
Jamhuriyar Dimukaradiyyar Congo dai sau biyu tana zama mamba a kwamitin daga shekarar 1982 zuwa 1983, sai kuma daga 1991 zuwa 1992, lokacin yaƙin Tekun Fasha.
A lokacin bikin ƙaddamar da gangamin da ya gudana a birnin Kinshasa, ministar harkokin wajen ƙasar Therese Kayikwamba Wagner, ta ce irin gogewar da ƙasar ke da ita da kuma la’akari da yadda take cikin sahun ƙasashen da suke karɓar bakuncin mafi yawan sojojin wanzar da zaman lafiya duniya, ta ke ganin ta cancanci samun kujerar a wa’adin zangon shekarar 2026 zuwa 2027.
Ta ce idan har ƙasarda ke Tsakiyar Afrika ta lashe zaɓen, za ta taka muhimmiyar rawa wajen tattauna batutuwan shirin ayyukan samar da zaman lafiya da kuma sauya fasalin yadda ake gudanar da shi.
Shi dai Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, shi ke da alhakin gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya a ƙasashe daban-daban,sannan kuma ya ke ɗaukar tsauraran matakai da doka ta amince masa da su na yin amfani da ƙarfin soji ko kuma sanya takunkumi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI