Sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar da Angola ke shiga tsakani an rattabata domin kawo ƙarshen rikicin dake tsakanin kasashen Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo da Rwanda.
Dukda karya yarjejeniyar tsagaita wutar da aka yi a shekarar 2021 masu shiga tsakani sun ci gaba da tattaunawa a wani yunkuri na kawo ƙarshe rikicin.
Bayanai sun tabbbatar da cewa ƙasashen na Congo da Rwanda sun sanya hannu kan yarjejeniyar ne domin yauƙaƙa alaƙar zaman lumana a tsakaninsu.
Tun a shekarar 2021 mayakan M23 da galibinsu ƴan Tutsi ne dake samun goyan bayan Kigali suka kwace iko da gabashin Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo, abinda ya mayar da dubban mutane ƴan gudun hijira tare da haddasa buƙatar tallafin jin ƙai a yankin.
A farkon watan Agusta Angola dake shiga tsakani ta yi nasarar fara farfaɗo da zaman lafiya a yankin, to amma tun a ƙarshen watan Octoban da ya gabata M23 ta ci gaba da kai farmaki.
To sai dai dukda karya ƙa’idar tsagaita wuta, Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo ta ci gaba da amincewa da tattaunawa a ƙoƙarin da Angola ta yi na kawo karshen rikicin.
A farkon watan Nuwamba ƙasashen biyu masu makwaftaka da Afirka ta Kudu suka amince a kafa kwamitin da zai lura da batun tsagaita wutar ƙarƙashin Angola da kuma wakilan Congo da Rwanda.
A ranar litinin ministocin wajen Kinshasa da Kigali suka amince da wata taƙadda da ta nuna cewar dakarun Rwanda za su fice daga iyakar Congo kamar yadda ministan harkokin waje na Angola ya tabbatar.
To sai dai gwamnatin Angola ba ta bada cikakken bayani kan yadda janyewar za ta kasance ba.
Sama da shekara 30 da suka wuce Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo dake da albarkatun ƙasa ke fama da rikice-rikice na cikin gida da na waje a yankin gabashi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI